Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa, rundunar sojin kasar, ta gano inda aka boye 'yan matan nan na makarantar Chibok, wadanda dakarun Boko Haram ke garkuwa da su, sai dai ba za su iya ceton su ba, saboda gudun asarar rayukan da hakan ka iya haddasawa.
Kamfanin dillancin labarun kasar ya rawaito babban kwamandan rundunar Alex Badeh na cewa, abin farin ciki ga iyalan yaran shi ne, an gano inda 'ya'yansu suke, sai dai ba zai yiwu a dauki matakin da zai haddasa kisan su ba da sunan ceto. (Saminu)