A yayin bikin, Mr. Li Yuanchao ya bayyana cewa, bikin nune-nunen hotuna ba abin tunawa kawai da dangantakar sada zumunci dake kasancewa tsakanin kasashen biyu ba, har ma ya kasance tamkar wani abin hangen nesa ne ga irin wannan dangantaka.
A nasa bangaren, Mr. Harry Kalaba, ministan harkokin wajen kasar Zambiya ya bayyana cewa, a lokacin da kasarsa take neman 'yancin kai, kuma cikin shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen Zambiya da Sin, kasar Sin ta kan tallafa wa kasar Zambiya. Jama'ar Zambiya ba za su manta da wannan ba.
A yayin bikin nune-nunen hotunan, an nuna yadda kasashen Sin da Zambiya suka yi kokarin bunkasa dangantakar sada zumunta tsakaninsu cikin shekaru 50 da suka gabata a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu, tarbiya, kiwon lafiya, wasannin motsa jiki da dai sauransu. (Sanusi Chen)