Kasar Tanzaniya ta bayyana fatanta a ranar Talata na tura kwararru a harshen Swahili a cikin kasashen yammacin Afrika, a cikin wani shirin da ya shafi baiwa wannan harshe muhimmin girma a nahiyar.
Da yake jawabi a zauren majalisar dokokin kasar Tanzaniya a Dodoma, hedkwatar kasar, ministar ilimin kasar Tanzaniya, madam Jenista Mhagama ta bayyana cewa, harshen Swahili ya samu babban cigaba a 'yan shekarun baya bayan nan, bisa ga yawan mutanen dake magana da wannan yare, ko kuma suke neman koyonsa.
A shekarar da ta gabata, shugaban kasar Gabon Omar Bongo ya bukaci kasar Tanzaniya da ta tura malaman da za su rika koyar da harshen Swahili a cikin jami'o'in kasarsa, in ji wannan jami'a. (Maman Ada)