in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a hukunta wadanda suka hallaka matashin 'dan Falasdinu, in ji shugaba Peres
2014-07-07 09:32:50 cri

Shugaban kasar Yahudawa ta Isra'ila Shimon Peres, ya ce, dole ne al'ummun Yahudawa da na Falasdinu, su gaggauta daukar matakan da suka wajaba domin kawo karshen takaddamar dake tsakaninsu ta hanyar lumana, a maimakon ci gaba da kaiwa juna hare-hare.

Peres wanda ya bayyana hakan a garin Sderotthe dake kudancin Isra'ila ya kara da cewa, gwamnatinsa na daukar matakan dakatar da hare-haren da take kaiwa yankunan zirin Gaza, matakin da a cewarsa, zai tabbata ne kawai, idan har aka daina kaiwa yankunan Yahudawa hari.

Hare-haren da bangarorin biyu dai ke kaiwa juna, ya biyo bayan zargin da ake yiwa wasu Yahudawa na kisan wani matashi Bafalasdine mai suna Mohammed Abu Khdeir, lamarin da shugaba Peres ya ce, tuni 'yan sanda suka fara bincike a kansa, da nufin tabbatar da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban shari'a.

Kalaman na shugaba Peres na zuwa ne, a gabar da jami'an tsaron kasar ke tabbatar da cafke wasu Yahudawa da dama a Shuafat dake gabashin birnin Jarusalem, bisa zargin kisan Abu Khdeir.

Kisan wannan matashi dai ya haddasa tashe-tashen hankula, sakamakon dauki ba dadin da jami'an tsaron Isra'ila ke yi da Falasdinawa masu zanga-zanga a Jerusalem, da ma wasu yankunan na daban. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China