in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci da a dakatar da rikicin Sudan ta Kudu
2014-07-09 10:56:26 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira a kan shugabannin Sudan ta Kudu da su koma kan teburin shawarwari nan take, tare da dakatar da rikici, wanda jama'a ne ke da alhakin haddasa shi.

Ban, ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa a yayin bikin zagayowar cika shekaru ukku, na samun 'yancin kai na kasar Sudan ta Kudu, Ban ya yi nuni da yadda jama'ar Sudan ta Kudu suka kasance cikin farin ciki da alfaharin fata na gari, a lokacin da kasarsu ta samu 'yancin kanta a ranar 9 ga Yulin shekara ta 2011.

Sudan ta Kudu, wacce ita ce jariyar kasa, ta fada cikin tashin hankali tun daga ranar 15 ga watan Disambar bara, a yayin da rikicin cikin gida tsakanin shugaban kasar Salva Kiir, da tsohon mataimakin shi Riek Machar, ya rikide ya koma wani babban rikici.

Kamar yadda MDD ta bayyana, karuwar rikicin ya haifar da jama'a miliyan 1 da rabi sun rasa muhallansu, tare da jefa wasu jama'ar miliyan 7 cikin barazana ta yunwa da kamuwa da cututtuka.

Sakatare janar na MDD ya tunatar da shugabannin Sudan ta Kudu cewar, suna da nauyi da ya hau kansu na tabbatar da cewar, sun dakatar da fadan da ake yi tare da aje makamansu a gefe guda, domin samun zaman lafiya a kasarsu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China