in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD na duba yiwuwar daukar karin matakai kan rikicin Sudan ta Kudu
2014-04-25 14:31:24 cri

Kwamnitin tsaro na MDD ya furta fushinsa game da tashin hankalin da aka yi kwanan nan a Sudan ta Kudu, inda aka kai farmaki a kan farar hula da kuma yankunan gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Kwamitin tsaron na MDD ya ce, zai duba yiwuwar daukar karin matakai idan aka ci gaba da kai hare-hare a kan farar hula.

Sanarwar kwamitin tsaron MDD, wadda aka rubuta da kalmomi masu zafi, ta fito ne daga mambobin 15 na kwamitin a karshen wata ganawa da suka yi da karamin sakataren ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD Herve Ladous, da kuma mataimakin sakataren MDD a bangaren kare hakkin bil'adama Ivan Simonovic a game da halin da ake ciki a Sudan ta Kudu.

Kwamitin tsaron ya fusata kwarai a game da mummunan tashin hankali da aka yi a Bentiu, a ranar 14 zuwa 16 ga watan Aprilu wanda ya haifar da hallaka fiye da mutane 200, wadanda suka hada da maza da mata da yara kanana.

Hakazalika mambobin kwamitin tsaron MDD sun kara nanata allah wadai din da suka yi da harin da ya haddasa asarar rayuka da jikkata jama'a, cikinsu hadda masu neman mafaka a sansanin na MDD, wanda aka kai a harabar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake Bor, a ranar 17 ga watan Aprilu.

Kwamitin tsaron ya kuma bukaci dukanin kungiyoyin da ke fada da juna a Sudan ta Kudu da su koma kan turbar samar da zaman lafiya a karkashin shiga tsakanin IGAD, kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China