Wasu manyan hukumomi na samar da taimakon agaji na duniya guda 7 sun yi kira da a taimakawa Sudan ta Kudu da dalar Amurka miliyan 89 domin kaucewa matsalar fari, da ke barazana ga kasar.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa, wacce aka bayar a yayin tunawa da bikin zagayowar ranar cika shekaru 3 na samun mulkin kan kasar Sudan ta Kudu, hukumomin agajin sun yi gargadi cewar, ayyukan da suke yi na taimakon agaji na fuskantar barazana saboda karancin kudi.
Alal misali, asusun Tearfund ya ba da rahoto cewar, idan aka kwatanta da shekarar bara, adadin yara da iyaye mata dake fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, ya karu har da ninki hudu a cibiyoyin ciyar da jama'a na asusun, guda shida dake cikin kauyukan kasar.
Rikicin na Sudan ta Kudu ya tilastawa mutane miliyan 1 da rabi barin gidajensu, kuma rikicin ya haddasa mutanen kasar kusan dubu 400, zamantowa 'yan gudun hijira a kasashe makwabta. (Suwaiba)