Mai ba da jagoranci ga tawagar Sin, kuma mataimakin hukumar al'adun birnin Beijing Madam Wang Zhu ta ce,
"Bunkasuwar dangantakar siyasa tsakanin kasashen biyu za ta kawo amfani wajen kara fahimtar juna tsakanin al'umomin biyu, kuma matakin da zai taimaka wajen karfafa hakan shi ne musayar al'adu. A ganina ta wannan hanya, jama'ar Sin da Afrika za su cimma burinsu na yin mu'ammala."
Wani matashi dan kasar Zimbabwe mai suna Danis, wanda ya kalli wannan biki ya bayyana farin cikinsa, yana mai cewa al' adun gargajiya na kasar Sin ya ba shi sha'awa kwarai, musamman ma fannin tufafi da fasahohi masu inganci, lamarin da ya sanya shi sha'awar zuwa birnin Beijing domin yawon bude ido. (Amina)