in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin nuna fasahohi da Sin ta gabatar a Zimbabwe ya samu matukar karbuwa
2014-07-17 17:00:52 cri

Ko da yake, salon da Peking Opera yake bi ya sha bamban sosai da fasahohin kasar Zimbabwe, amma masu kallo a kasar Zimbabwe sun nuna sha'awa kwarai kan wannan fasahar gargajiya daga gabas. Ban da Peking Opera, masu fasaha na kasar Sin sun yi wasannin lankwasa jiki, wadanda suka sami lambobin yabo a duniya.

Shugabar kungiyar wasannin lankwasa jiki Madam Zhang Hong ta ce,

"Mun kwashe tsawon lokaci muna shirya wadannan ayyuka, wasu fasahohin da muka gabatar mun yi su ne domin wannan biki. Bisa hadin kai da muka yi da kwalejin Confucius, da kwalejin koyar da ilmi kide-kide da wake-wake a Zimbabwe, mun gabatar da wadannan ayyuka masu inganci. Hudu daga cikinsu sun sami lambobin yabo masu armashi a duniya."

Abin da ya fi ba da mamaki shi ne, an hada al'adun Sin da Afrika tare a cikin wasu ayyuka da aka yi cikin bikin. A nata bangare mai nuna wasa da abin kida na Pipa madam Zhang Hongyan, daga babban kwalejin koyar da ilmin kide-kide da wake-wake ta kasar Sin, ta gabatar da wata shaharariyar waka ta al'ummar Zimbabwe da abin kida na Pipa, wani kayan kida na gargajiya na kasar Sin.

A nata bangare kuwa, kungiyar mawaka ta kwalejin Zimbabwe, da ta kwalejin Confucius sun rera wata waka mai suna "Kiyaye tsaron rawayen kogi" da Sinanci, da kuma wata waka da suka tsara mai suna "Ina son in je Beijing." wasannin da suka yi cikin hadin kai sun sami karbuwa da yabo sosai daga masu kallo.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China