in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin nuna fasahohi da Sin ta gabatar a Zimbabwe ya samu matukar karbuwa
2014-07-17 17:00:52 cri

Gwamnatin birnin Beijing da ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe ne suka yi hadin gwiwar gabatar da wannan biki da aka yi wa lakabi da "Daren birnin Beijing". Inda shugabar tawaga ta farko ta Peking Opera Madam Wang Rongrong wadda ta yi suna wajen nune-nunen Peking Opera, ta gabatar da wasan kwaikwayo mai suna "Matar sarki ta yi bugu". Haka nan tawagar 'yan wasan nuna asahohi daga cibiyar Peking Opera na birnin Beijing, sun yi kokarin bayyana kwarewarsu a fannoni daban-daban. Har ma Madam Wang Rongrong ta bayyana cewa,

"Duk lokacin da 'yan kasashen waje suka ambaci fasahohin gargajiya na kasar Sin, ana tunawa da Peking Opera. Wanda hakan ke bayyana tunani mai zurfi, da fasahohi da dama kamar rera waka, da karanta kalmomi bisa wake-wake, da raye-raye masu salon Peking Opera da wasan Kungfu. Wasan da ya sabawa sauran fasahohi na kasashen waje kamar rawar Ballet, da ba ta dauke da waka. Haka fasahar mashahurin mawakiyar nan mai suna Luciano Pavarotti, fasaha ce ta rera waka ba tare da wasan kwaikwayo ba. A hannu guda wasan "Peking Opera" ya hada wadannan fasahohi tare, wanda hakan ya sanya shi samun karbuwa da janyo hankali mutane."

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China