Sabon zagayen shawarwarin nufin kawo karshen yajin aiki na ma'aikatan mahakar ma'adinan karfen Platine a Afrika ta Kudu ya kammala ba tare da cimma wani sakamako mai kyau ba.
Shawarwarin, an yi su ne tsakanin kungiyar ma'aikatan ma'adinai da kungiyar gine-gine (AMCU), da kuma manyan kamfanonin samar da karfen Platine uku a yayin da mambobin kungiyar AMCU dubu 80 sun kaucewa aiki tun ranar 23 ga watan Janairu domin nuna goyon baya kan bukatunsu na karin albashi.
A yayin jerin tattaunawar baya bayan nan, bangarorin biyu sun kasa cimma wata yarjejeniya kan muhimman batutuwa, amma duk da haka sun amince da sake komawa teburin shawarwari a mako mai zuwa, bayan hutun Paques wato Easter Day, a cewar wasu majiyoyi masu tushe na kusa da wadannan shawarwari. (Maman Ada)