in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Syria ya jaddada muhimmancin kafa kawancen kasa da kasa domin yaki da ta'addanci
2014-01-20 10:56:46 cri

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya bayyana a ranar Lahadi, wajabcin kafa wani kawancen kasa da kasa domin yaki da ta'addanci, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar SANA.

Mista al-Assad ya yi wannan furuci a yayin wata ganawa da tawagogin addini da na 'yan majalisar dokokin kasar Rasha dake cikin wata ziyarar aiki a birnin Damascus.

Shugaba al-Assad ya bayyana muhimmancin tunkarar wadannan kungiyoyin kishin islama ta hanyar daukar matakai masu tsanani da wajabcin kafa wani kawancen kasa da kasa domin yaki da ta'addanci da kuma kafa wani kawancen addinin muslumci domin dakatar da yunkurin masu kaifin kishin addini.

Gwamnatin Syria ta bayyana cewa, tana yaki da gungun kungiyoyin ta'addanci dake da alaka da kungiyar Al-Qaida da kuma wasu mutanen dake da alaka da wadannan kungiyoyi.

Haka kuma gwamnatin Syria ta bayyana cewa, yaki da ta'addanci shi ne mataki na farko wajen warware wannan rikici ta hanyar siyasa da kasar take fama da shi yau da kusan shekaru uku.

Mista al-Assad ya yi kashedi cewa, matsalar ta'addancin da Syria take fama da ita na iyar zama wata barazana a shiyyar gaba daya.

A ranar lahadi, faraminstan kasar Syria Wael al-Halqi a yayin wata ganawa da tawagar 'yan majalisun kasashen yammacin duniya, ya nuna cewa, ya kamata kasashen yammacin duniya su daina matsin lamba kan gwamnatin kasar Syria tare kuma da yin kira gare su da su daina tallafawa 'yan ta'adda dake Syria. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China