in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta jaddada muhimmancin shigar wakilan 'yan adawar gida zaman shawarwarin da ake yi
2014-02-19 10:37:33 cri

Kakakin majalisar dokokin kasar Sham Gihad Laham, ya jaddada muhimmancin shigar wakilan 'yan adawar kasar na cikin gida, tattaunawar da ake yi da tsagin gwamnati, da nufin shawo kan matsalolin siyasar kasar.

Laham wanda ya bayyana hakan a ranar Talata 18 ga watan nan, yana mai cewa, mahukuntan kasar na burin ganin an shigar da 'yan adawar dake cikin gida cikin tattaunawar da ake yi a gida da waje, musamman ganin yadda suke kokarin ba da gudummawar kamo bakin zaren takaddamar dake gudana yanzu haka a kasar, sabanin abin da ake gani daga wakilan 'yan adawa dake gudun hijira ko SNC a takaice.

Wakilan tsagin 'yan adawar dake gudun hijira ko SNC ne dai suka wakilci 'yan adawar kasar ta Sham, yayin tattaunawar farko da ta biyu da aka yi a birnin Geneva, matakin da ya sanya ragowar 'yan adawar dake gida rasa wakilci. Don gane da hakan ne NCB, daya daga kungiyoyin 'yan adawar dake cikin kasar ta Sham, suka zargi kasashen yamma da nuna musu wariya.

Yanzu haka dai 'yan adawar cikin gidan kasar ta Sham na ci gaba da kiraye-kiraye, na ganin an ba su damar shiga a dama da su, a zaman tattaunawar birnin Geneva karo na biyu. Hakan kuma na zuwa ne a gabar da aka yanke kudurin gudanar da zaman tattaunawa karo na uku, tsakanin wakilan gwamnatin Sham da na SNC, ko da yake dai ba a ayyana lokacin gudanar zaman ba.

Yayin tattaunawar da sassan biyu suka yi a baya dai, tsagin gwamnatin Sham ya mai da hankali ga batun dakatar da tashe-tashen hankula, da yaki da ta'addanci, yayin da SNC ta kafe kan cimma yarjejeniyar kafa hukumar rikon kwaryar kasar, wadda babu hannun shugaba Bashar al-Assad cikin gudanar ta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China