Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramtane Lamamra, ya ce, an gudanar da musayar firsinoni tsakanin mahukuntan kasar Mali da tsagin 'yan tawaye dake da sansani a arewacin kasar, karkashin kulawar wakilan kasar Aljeriya.
Mr. Lamamra wanda ya bayyana hakan gabanin taro na 5, na hadin gwiwa tsakanin kasashen Aljeriya da Mali da ya gudana a ranar Talata, ya kuma kara da cewa, musayar firsinonin, ta kunshi sakin mutane 45 daga tsagin 'yan tawayen, da kuma wasu mutane 42 daga bangaren mahukuntan kasar.
Kaza lika ministan harkokin wajen kasar ta Aljeriya ya ce, tuni aka bude zaman tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin ta Mali, da na mayakan sakan kasar a birnin Aljiyas, a wani yunkuri na kawo karshen tashe-tashen hankula, da fada tsakanin bangarorin biyu ke haddasawa.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan da bangarori 3 na 'yan tawayen Malin suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya, da ta tanaji hawa teburin shawara, da nufin zakulo hanyoyin magance matsalolin tsaro a arewacin kasar. (Saminu)