in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a goyi bayan shirin wanzar da zaman lafiya a Mali
2014-06-16 09:50:22 cri

Babban jami'in shirin farfado da zaman lafiya na MDD a kasar Mali Albert Gerard Koenders, ya yi kira da a dauki karin matakan wanzar da zaman lafiya a kasar, ta hanyar shigar da daukacin masu ruwa da tsaki cikin tsare-tsaren kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Mr. Koenders ya yi wannan kira ne yayin ziyarar da ya kai kasar ta Mali a jiya Lahadi. Jami'in ya kara da cewa, tattaunawar baya bayan nan da aka yi a birnin Aljiyas tsakanin bangarorin kasar ta Mali biyu, na da muhimmancin gaske, wajen cimma burin da aka sanya gaba.

Daga nan sai ya yi fatan ganin daukacin bangarorin kasar sun rungumi shirin tattaunawa ba tare da bata lokaci ba, tare kuma da daukar matakan dawo da yanayin zaman lafiya da lumana a fadin kasar baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China