in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS za ta dauka nauyin shirin gyare-gyaren yankin tsaunukan Fouta Djallon
2014-07-16 09:33:49 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta mika wa gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) a ranar Talata aikin aiwatar da wani shirin gyare-gyaren yankin tsaunukan Fouta Djallon, bisa wata yarjejeniyar da aka cimma a birnin Conakry na kasar Guinea.

Wannan shirin ya shafi kasashe takwas dake cin gajiyar ruwan dake fitowa daga yankunan tsaunukan Fouta Djallon, wadanda suka hada da Guinea, Guinea-Bissau, Gambiya, Mali, Mauritaniya, Nijar, Senegal da Sierra-Leone.

Makasudin wannan shirin shi ne don tabbatar kariya da amfani cikin daidaici da albarkatun ruwa da muhalli na yankin tsaunukan Fouta Djallon, ta yadda za'a iyar taimakawa ga kyautata zaman rayuwar al'ummomin a wadannan yankuna da ruwan Fouta Djallon ke ratsawa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China