Annobar cutar Ebola da yanzu haka take addabar kasashen Sierra-Leone, Liberiya da Guinea, za ta kasance daya daga cikin manyan batutuwan da za'a tattauna a yayin babban taron kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) karo na 45 da aka tsai da yin sa a ranakun Alhamis da Jumma'a a birnin Accra na kasar Ghana.
Shugabannin kasashen shiyyar yammacin Afrika za su kuma yi shawarwari kan kudurin shigar da takardun katin 'dan kasa na zamani masu amfani da kwayoyin halitta ga dukkan al'ummar kungiyar ECOWAS, da kuma soke bukatar lasin zama da dukkan mazauna kasashe mambobin wannan kungiya, in ji wata sanarwa ta fadar shugaban kasar Ghana a ranar Litinin.
Shugaban kasar Ghana John Dramini Mahama zai shirya wannan dandali, a matsayinsa na shugaban kwamitin koli na shugabanni da gwamnatocin kasashen mambobin kungiyar ECOWAS.
Haka kuma taron zai mai da hankali kan rikicin kasar Guinea-Bissau, inda sabon shugaban kasar ya yi rantsuwar kama aiki a watan da ya gabata bayan kasar ta shirya zabubukan 'yan majalisa da shugaban kasa cikin nasara tare da taimakon kungiyar ECOWAS. (Maman Ada)