in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS za ta fara amfani da haraji na bai daya a shekarar ta 2015
2014-07-11 10:43:10 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ce, ana sa rai hukumar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, za ta fara amfani da haraji na bai daya, daga ranar daya ga watan Janairun shekara ta 2015.

Shugaban kasar ta Ghana, wanda yanzu shi ne ke shugabantar hukumar ta ECOWAS, ya bayyana hakan ne a yayin da ya bude zaman taro, a karo na 45, na hukumar tattalin arzikin ta kasashen yammacin Afrika.

A shekarar 2006 ne shugabannin da gwamnatocin kasashen hukumar ta ECOWAS, suka yanke shawarar kafa wani tsari na bai daya na biyan haraji a karkashin rukuni 4, na kayayyakin da ake shiga da su kasashensu, da zimmar share hanya na kulla yarjejeniyar huldar tattalin arziki da kungiyar tarayyar Turai EU.

Taron na ECOWAS ya samu halarcin shugabannin kasashe 15 da kuma tawagar kasashe makwabta, tare da wakilai daga MDD da kuma kungiyar tarayyar hadin kan Afrika AU. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China