Kwamishinan ma'aikatar lafiya na jihar Lagos ta tarayyar Najeriya Mr. Jide Idris ya ce, birnin Lagos zai ci gaba da kasancewa a shirye domin hana kwayar cutar Ebola mai saurin yaduwa, shiga cikin birnin dake kudu maso yammacin kasar.
Wata sanarwar ma'aikatar lafiya, wacce ta isa hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ta ce, kwamishinan lafiyar na jihar Lagos ya shawarci jama'a da su kasance masu tsabtace jikinsu, da kuma muhallansu a matsayin matakan taka tsan-tsan na hana yaduwar cutar Ebola a jihar.
Kwamishinan lafiya Jide Idris ya yi nuni da cewar, ba da shawara ya zama dole saboda karuwar yawan adadin wadanda suka kamu da cutar, da kuma karuwar adadin wadanda suka mutu, a sakamakon cutar a wasu kasashe makwabta dake yammacin Afrika, wadanda suka hada da Guinea, Liberira da Saliyo.
Kwamishinan ya jaddada cewar, kawo ya zuwa yanzu babu wani takamaiman maganin cutar ta Ebola, wacce tana iya yaduwa a yayin da ake kulawa da wadanda suka kamu da cutar. (Suwaiba)