Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bukaci mahukuntan kasar Libya da su shirya gudanar da zaben 'yan majalissar dokokin kasar a kan lokaci. Mr. Ban ya kuma yi kira da a dauki dukkanin matakan da suka wajaba, musamman ma matakan da za su dace da muradun al'ummarta, wajen shawo kan dambarwar siyasar kasar.
Wata sanarwa da kakakin babban magatakardar MDDr ya fitar, ta jaddada muhimmancin ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNSMIL, wadda ke ba da tallafin kwararru a fannin sake farfadowar kasar. Daga nan sai Ban ya yi kira da a rungumi hanyar siyasa, a matsayin kafar magance matsalolin kasar, tare da dora ta kan turba ta gari.
An dai tsara gudanar da zaben 'yan majalissar kasar ta Libya ne a ranar 25 ga watan Yunin nan, bayan da a baya aka rika dade zaben sakamakon rashin samun cikakken kwanciyar hankali a siyasance.
Bisa tsarin mulkin kasar dai sabbin zababbun 'yan majalissar wakilan kasar ne, za su maye gurbin 'yan majalissar wucin gadi masu ci a yanzu. (Saminu)