in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO za ta kafa cibiyar dakile cutar Ebola a Guinea
2014-07-04 10:36:10 cri

Darektan hukumar lafiya ta duniya WHO a Afrika, Dr. Luis Gomes Sambo, ya ce, nan ba da dadewa ba hukumar za ta kafa cibiyar hana yaduwar cutar Ebola a kasar Guinea.

An yanke shawarar kafa cibiyar ne, a sakamakon shawarwarin wani taro a kan cutar Ebola, wanda ya samu halarcin ministocin lafiya na kasashen yammacin Afrika , da kwararru na kasashen waje.

Dr. Sambo ya ce, hukumar lafiyar ta duniya tana sa rai ma'aikatan kimiyya da abin ya shafa da abokan hulda masu bayar da taimakon kudade, za su hada hannu wuri guda a wannan hadin kan, domin zaburar da kokarin da ake yi na dakile cutar ta Ebola.

Cibiyar da za'a kafa, za'a yi mata lakabi da cibiyar dakile cutar Ebola a Guinea Conakry.

Taron ya nuna mahimmancin jagoranci a kowane mataki, tare da yin kira a kan shugabannin kasashe da na gwamnatoci, da su hada hannu wajen samar da kudaden da ake bukata, tare da inganta shirye-shiryen da aka tsara, domin murkushe cutar ta Ebola mai saurin yaduwa, wadda har yanzu ba ta da magani. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China