Mamba a majalisar zartaswa ta kasar Sin, Yang Jiechi ya gana da ministan harkokin waje na kasar Uganda Sam Kutesa a birnin Beijing, a jiya Laraba, a inda suka yi musayar ra'ayi akan hulda tsakanin Sin da Uganda da kuma halin da ake ciki a nahiyar Afrika.
Yang ya ce, kasar Sin tana girmama rawar da Uganda ke takawa a yankin Afrika, da kuma tasirin da take yi a al'amuran duniya.
Yang ya kara da cewar, kasar Sin a shirye take ta dauki wani matakin hadin gwiwa da kasar Uganda, tare da kara dangantaka ta ko wane fanni, kamar dai yadda yarjejeniyar, da aka cimmawa tsakanin shugaban kasar Sin, Xi Jinping da shugaban kasar Uganda, Yoweri Kaguta Museveni ta tanadar.
A nashi bangaren, ministan harkokin wajen Ugandan Mr. Kutesa, ya yaba kwarai da hulda dake tsakanin Uganda da Sin, a inda kuma ya nuna jin dadinsa game da kokarin da kasar Sin ke yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin tare da bayar da tallafi wajen habbaka kasashen Afrika. (Suwaiba)