in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Palasdinawa za su tuntubi MDD don dakatar da harin Isra'ila
2014-06-23 13:34:03 cri

Shugabannin Palasdinawa sun yanke hukuncin tuntubi kwamitin tsaro na MDD, domin kwamitin ya dakatar da matakan harin da Isra'ilar ke dauka a kan yankunan Palasdinawa, kamar yadda suka ce, hare-haren Isra'ila sun karu tun bayan bacewar wasu matasa 3, 'yan kasar ta Isra'ila a ranar 12 ga watan Yuni a kusa da yammacin gabar kogin Jordan.

A cikin wata sanarwa da aka baiwa manema labarai, shugabannin Palasdinawan sun ce, sun tuntubi kwamitin tsaron MDD domin ya gudanar da taron gaggawa, da zimmar dakatar da abin da aka kira hare-haren mugunta da ake kaiwa Palasdinawa.

Shugabannin na Palasdinawa sun kunshi manyan mambobin kungiyar ceton Palasdinawa da kuma mambobin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Fatah.

Al'amurran tsaro a yammacin kogin Jordan sun tabarbare tun bayan bacewar matasan Isra'ila, to amma kuma tuni kungiyar Hamas ta ce, ba ta da alhakin sace matasan 3, 'yan kasar Isra'ila, a inda kuma ta zargi Isra'ila da sharara karya.

Tun bayan bacewar matasan sojojin Isra'ila sun kashe Palasdinawa 5, tare da kame wasu Palasdinawa 400. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China