in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Faransa sun amince da kafa wani tsari na musayar al'umma
2014-03-27 12:31:05 cri

A ranar Laraba ne kasashen Sin da Faransa suka amince su girka wani babban tsarin musayar al'adu da jama'ar juna, domin habbaka huldar sadarwa da gamayya da juna tsakanin kasashen biyu a bangaren harkokin ilmi dana al'adu.

An cimma wannan yarjejeniyar ne a yayin tattaunawa tsakanin shugaban kasar Sin, Xi Jinping, wanda ya kai ziyara a Faransa da takwaransa na kasar Faransa Francois Hallande. Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin dake akwai, na ci gaba da kara zaburar da fahimtar juna tsakanin al'umomin kasashen biyu, a yayin da dukanin kasashen biyu ke gudanar da bukukuwa na cika shekaru hamsin da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, a wannan shekarar da muke ciki.

Shugaban kasar ta Sin yana Faransa ne, domin kai wata ziyarar aiki, a sakamakon gayyatar da ya samu daga takwaran shi Hollande. A yayin wannan ziyara, Xi, zai halarci bukukuwan murnar cika shekaru hamsin na kulla huldar diplomasiyya tare da ganawa da firaministan kasar Faransa, Jean-Marc Ayrault da kuma shuwagabannin majalisun tarayyar kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China