in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta jinjinawa ayyukan kiyaye zaman lafiya na Algeriya a Sahel
2014-06-09 10:58:00 cri

Ministan harkokin waje na Faransa, Laurent Fabius, jiya Lahadi ran 8 ga wata ya ce, kasarsa da Algeriya sun yi alkawarin aiki tare domin murkushe ta'addanci a yankin Sahel dake Afrika, musamman rikicin da ya addabi kasar Mali.

Ministan Faransan wanda ya kai ziyarar kwanaki 2 a Algeriya ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai, da ya harlarta tare da ministan harkokin wajen Algereiya, Ramtane Lamamra.

Ministan na Faransa ya ce, babu wani ci gaba, idan babu tsaro, ya kuma jaddada bukatar dake akwai, na ci gaba da aiki tare domin tunkarar yakin da suke yi da ta'addanci.

Ministan harkokin wajen Algeriya Lamamra, ya ce, Algeria, wacce ke arewacin Afrika, ta gudanar da gagarumin kokari na girka tsaro a kan iyakokinta domin kare su daga barazanar 'yan ta'adda, ya kara da cewar, kasarsa a shirye take, ta kawar da 'yan ta'adda daga yankin.

Kasar Mali, ta fada cikin rudanin tashin hankali, a cikin 'yan shekaru, bayan wani juyin mulki a Bamako, da kuma barkewar wani rikici a arewacin kasar, wanda ya yi sanadiyyar kungiyoyin kabilar Tuareg suka yi shelar ballewa daga kasar ta Mali, kuma daga bisani wadansu kuingiyoyi masu tsatsauran ra'ayi, suka kwace iko a yankin.

Makwabciyar kasar Algeriya daga sashen gabashin kasar, Libya, ita ma tashin hankali da rikicin siyasa suka mamaye ta tun bayan faduwar gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011, wannan ya sa Algeriya ta tura dakaru domin gadin kan iyakarta da Mali, da kuma gudanar da kokari na murkushe 'yan tsagera da kuma masu fasa kwaurin makamai. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China