Babbar darekta mai kula da ofishin mata a MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka ta tabbatar wa Nigeriya da goyon bayan majalisar a kan ilimin 'ya'ya mata a kasar, lokacin da ta ziyarci kasar a cikin wani shiri na nuna goyon baya ga kasar, da kuma jajanta mata tare da iyalan 'yan matan da aka sace.
Kamar yadda kakakin majalissar Stephane Dujarric ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin din nan, ziyarar madam Mlambo-Ngcuka ta zo ne a daidai lokacin da ilimin 'ya'ya mata yake fuskantar barazana saboda fargaban harin 'yan Boko Haram a makarantu, kungiyar 'yan ta'adda masu ikirarin son shimfida shari'ar musulunci a kasar.
A lokacin ziyararta a makarantar gwamnatin tarayya dake garin Abaji, madam Mlambo-Ngcuka ta tabbatar da goyon bayan MDD cewa, za ta yi aiki tare da gwamnati wajen ganin karatun 'ya'ya mata bai samu koma baya ba.
Babbar darekta a MDD ta kuma yi kokarin cire duk wani zulumi dake tare da iyaye na tura yaran su makaranta. (Fatimah)