in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kerry ya tabbatar da inganta zumunci tsakanin Amurka da Sin a ziyararsa mai zuwa
2014-02-10 16:08:02 cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya tabbatar da cewa, ziyararsa dake tafe zuwa kasar Sin za ta kara inganta zumunci tsakanin kasashen biyu.

A cikin sanarwar da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Jen Psaki ta fitar a ranar Lahadin nan, an ce, a ranakun 13 zuwa 18 ga watan nan John Kerry zai kai ziyarar aiki a kasashen Sin, Korea ta Kudu, Indonesia, da Hadaddiyar Daular Larabawa.

A lokacin ganawar da jami'an kasar Sin, Mr Kerry zai isar da sakon cewa, Amurka na da cikakken burin ganin an samar da sakamako mai armashi da hadin gwiwwa da ingantaccen ci gaba, kuma tana maraba da daukaka zaman lafiya da cigaban da kasar Sin take koyarwa a ko da yaushe cikin al'amurran duniya.

Babban jami'in na Amurka zai kuma tattauna batutuwan da suka shafi yankuna, kamar na kasar Koriya ta Arewa, da kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin Sin da Amurka a bangaren sauyin yanayi da samar da makamashi mai tsabta.

A Seoul, babban birnin kasar Koriya ta Kudu, Mr. Kerry zai jaddada muhimmancin da ke cikin hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu da kuma hada kai domin sasantawa da Koriya ta Arewa. A Jakarta, babban birnin kasar Indonesiya, sakataren harkokin wajen Amurkan zai gana da Li Luong Minh, babban magatakardar kungiyar kasashen kudu maso gabashin yankin Asiya, in ji Psaki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China