in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea da Mali za su kafa rukunin jami'an tsaron kan iyakokinsu domin karfafa tsaro
2014-07-10 10:42:37 cri

Kasashen Mali da Guinea, sun kafa wani rukunin jami'an tsaro na kan iyakokinsu dake kunshe da mambobi goma sha hudu a yankunan Kouremali, Siguirini da Nyagassola, da zummar kara karfafa matakan tsaro da zaman lafiya a wannan yanki.

Kafa wannan rukuni na bisa tsarin manufar kungiyar hadin kan kogin Mano, a matsayin wata hukumar wannan shiyyar da ta hada kasashen Guinea, Liberiya, Cote d'Ivoire, Sierra Leone.

Kasar Guinea da kasar Mali da ba ta cikin kungiyar hadin kan kogin Mano, na raba kan iyakoki guda, inda wasu lokuta ake samun rikicin filayen noma tsakanin al'ummomin kasashen biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China