Majalisar dokokin kasar Benin ta cimma wata dokar game da manufar daidaita sana'ar kamun kifi, a cewar wata majiya mai tushe daga wannan hukuma.
A cewar wasu matakan wannan doka kan sana'ar kamun kifi, wasu ayyuka da hanyoyin da ake bi wajen kamun kifi, za'a hana su. Dokar ta shafi wasu injunan da ake amfani da su a wasu lokuta domin kamun kifi dake janyo illa ga muhalli da ruwa da kuma janyo bacewar kifaye, da kuma hana amfani da raga wajen kamun albarkatun ruwa. Haka kuma an hana amfani da injunan da aka hada da raga wajen kamun kifi. (Maman Ada)