A lokacin ganawarsu, shugaba Xi ya ce bankin duniya ya kasance abokin kasar Sin mai muhimmanci, musamman ma a fannin neman ci gaban kasar, ganin yadda bankin da kasar Sin suke hadin gwiwa yadda ya kamata yayin da kasar ta Sin take kokarin aiwatar da gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.
A nasa bangaren, mista Jin Yong ya ce bankin duniya na gode ma kasar Sin kan gudunmowar da ta samar mata a kan gyare-gyare da ayyukan harkar rage talauci a duniya.
Haka kuma duk a wannan rana, firaministan kasar Sin mista Li Keqiang shi ma ya gana da mista Jin Yong, inda suka yi musayar ra'ayi kan kwaskwarima dake gudana a kan tsarin likitanci na kasar Sin. (Bello Wang)