in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da ba da taimakon agaji a Sudan ta Kudu
2014-07-02 10:51:03 cri

Ofishin MDD mai kula da al'amurran taimakon agaji OCHA ya ce, duk da kasancewar barazanar karancin tsaro, ana ci gaba da gudanar da ayyukan taimakon agaji, kamar yadda aka saba a Bentiu, babban birnin kasar Sudan ta Kudu.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai cewar, hukumomin agaji na ci gaba da inganta samar da ruwan sha, da tsabtacen muhalli, ta yadda, a yanzu an samawa kowanen 'yan gudun hijira 100, dake zaune a cibiyoyin kulawa na MDD, wurin ba haya guda daya, domin amfanin su, kuma ana ba kowanensu lita bakwai na ruwa.

Dujarric ya kara da cewar, hukumomin MDD suna da muradin agazawa 'yan gudun hijira miliyan 3.8 nan da zuwa karshen wannan shekarar, kuma a yanzu mutane miliyan 1.9 a fadin Sudan ta Kudu, tuni sun sami taimakon agaji a wannan shekarar.

Rikicin siyasa tsakanin shugaban kasar Salva Kiir, da tsohon mataimakinsa Riek Machar, ya rikide ya koma wani babban rikici, wanda ya haddasa asarar dubanin rayukan jama'a, tare da haifar da 'yan gudun hijira kusan miliyan 5, dake bukatar taimakon agaji, hakan ya sa ana ci gaba da aikata ba daidai ba, a dukanin bangarorin dake adawa da juna.

Wani adadi daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR na nuni da cewar, 'yan Sudan ta Kudu fiye da dubu 923 ne suka rasa muhallansu a cikin kasarsu, kuma a lokaci guda, fiye da 'yan kasar ta Sudan ta Kudu sama da dubu 293, suka zama 'yan gudun hijira a kasashe makwabta tun bayan da aka fara rikicin a tsakiyar Disambar shekarar 2013. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China