A jiya Laraba ne aka kaddamar da bikin shekarar kasar Afirka ta Kudu a birnin Beijing na kasar Sin, inda ake sa ran za a nuna majigin gwagwarmayan neman 'yancin kan kasar a wani lokaci a nan kasar Sin.
Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Afirka ta Kudu Wei Xin ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai a birnin Pretoria.
Ya ce, bikin yana da muhimmanci a bangaren aikin musayar abokantaka tsakanin kasashen biyu wanda ke nuna irin ayyukan musaya na abubuwan da sassan biyu suka koya daga juna, wadanda suka hada da fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya, al'adu, harkokin talabiji da fina-finai, ilimi da kuma yawon shakatawa.
Yayin bikin wannan shekara na kasar Afirka ta Kudu, ana sa ran a gudanar da shagulgula sama da 50, kamar bunkasa harkokin al'adu, musayar kayayyakin hannu, baje kolin kayayyakin cinikayya, tarukan karuwa juna sani na masana da musayar ilimi.
Kimanin sama da mutane 1500 ne ciki har da wakilan sassa daban-daban na rayuwa da ke Sin da na ofisoshin jakadancin Afirka da ke Sin ne suka halarci bikin. (Ibrahim)