Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) za ta kira wani babban taron ministocin kiwon lafiya na kasashe 11 a ranakun 2 da 3 ga watan Juli a birnin Accra domin bullo hanyoyin magance annobar cutar Ebola dake cigaba da yaduwa a kasashen Guinea, Laberiya da Sierra Leone.
Kungiyar WHO ta ba da gudunmuwa ya zuwa wannan lokaci na kayayyaki ta hanyar tura tawagogin kwararru da likitoci fiye da 150, da kuma gudanar da wasu ayyuka domin fuskantar wannan annobar wadanda suka hada da sanya ido, fadakarwa da janyo hankalin jama'a, sanya ido kan yaduwar cutar da sauransu.
Duk da wannan kokari, yawan mutanen da kamuwa da cutar Ebola na cigaba da karuwa, haka kuma an gano wasu sabbin yankunan dake fama da wannan bala'in a makwanni uku da suka gabata.
Ya zuwa ranar 23 ga watan Yuni, mutane 635 suka kamu da wannan cutar, daga cikinsu 399 sun kwanta dama. (Maman Ada)