Sabon zababben shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya umarci firaministan kasar Ibrahim Mahlab da kafa sabuwar majalissar zartaswa, bayan da a baya Mahlab din ya mika takardar murabus, domin baiwa sabon shugaban kasar damar zabar mataimakansa.
Kamfanin dillancin labarun kasar ta Masar ya bayyana cewa, yanzu haka Mahlab zai jagoranci majalissar zartaswa ta rikon kwarya, wadda za ta kunshi tsaffin ministocin kasar, ya zuwa lokacin da za a kammala zabukan 'yan majalissar kasar baki daya. A wani mataki da zai zamo na karshe cikin jerin kudurorin sauyi da sojoji suka tsara bayan tsige Morsi daga kujerar shugabancin kasar.
Bisa kuma tsarin mulkin kasar ta Masar na shekarar 2014, za a yi amfani ne da tsarin shugaban kasa, da zai baiwa firaminista iko mai yawa a harkokin zartaswa. (Saminu)