Sakataren wajen Amurka John Kerry ya tattauna da zababben shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, a birnin Alkahira, fadar gwamnatin Masar. Ziyarar ta ranar Lahadi ta kasance irinta ta farko da wani babban jami'in Amurka ya kai kasar, tun bayan darewar Sisi kujerar jagorancin kasar a farkon watan nan.
Yayin zantawar tasu, Kerry ya yaba da irin goyon baya da shugaban na Masar ya nuna, game da batun hadin gwiwar warware matsalolin siyasar yankin Gabas ta Tsakiya, da ya kunshi matakan kawo karshen tashe-tashen hankula a Iraqi da Sham da kuma kasar Libya. Kaza lika sakataren wajen na Amurka ya jaddada goyon bayan kasarsa ga Masar, yana mai cewa, shugaba Obama na fatan yin aiki kafada da kafada da Sisi.
Kafin ganawar tasu dai sai da Kerry ya zanta da takwaransa na Masar Sameh Shoukry, inda daga bisani kuma suka gudanar da taron manema labaru na hadin gwiwa. Inda Shoukry ya bayyana cewa, alakar dake tsakanin Amurka da Masar na da muhimmancin gaske a fannin cimma moriyar juna, da girmama juna, tare da kare muradun bangarorin biyu a fannin diflomasiyyar kasa da kasa.
Masu fashin baki dai na ganin wannan ziyara ta Kerry a Masar, ba ta rasa alaka da kokarin gwamnatin Amurka na karfafa dangantaka da sabuwar gwamnatin kasar ta Masar. (Saminu)