Nicholas Kay, babban jami'in MDD dake kasar Somalia a ranar Talata, ya yi kakkausar suka a kan kashe wani 'dan majalisar dokokin kasar Abdelaziz Isaq Mursal, wanda kuma ya zamanto 'dan majalisa na biyu da aka kashe a cikin awoyi 48, a fadar babban birnin kasar Mogadishu, in ji kakakin MDD Stephane Dujarric.
Wakilin na musamman na babban sakataren MDD, Nicholas Kay a Somalia ya ce, yana jimamin hare-haren da aka kai na baya bayan nan a Mogadishu, a inda kuma ya gabatar da kira a kan hukumomin kasar da su gudanar bincike, tare da tabbatar da karin kaimin gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata laifin a gaban hukuma. Kamar dai yadda kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyanawa manema labarai, wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba su ne suka harbi Abdelaziz Mursal a ranar Talata, bayan rasuwar Isaq Mohammed Riino, wanda aka kashe a ranar Litinin a yayin da wani abu ya fashe a motarsa.
Yayan kungiyar Islama ta Al-Shabaab sun ce su ne suka kashe 'yan majalisar dokokin, kuma sun sha alwashin cewar, za su ci gaba da kaiwa jami'an gwamnatin Somalia hare-hare.
Kay ya ce, masu aiwatar da wadannan miyagun laifuka ba su da wani abu illa tada hankalin jama'ar Somalia da kawo cikas ga harkoki na tsaro a kasar. Kay ya nuna rashin jin dadinsa ga matakin da aka dauka na harbi wani ma'aikacin kafofin watsa labarai a daren jiya, Kay ya kara da cewar, dole ne a baiwa kafofin watsa labarai damar gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba. (Suwaiba)