Sabon jakadan kasar Sin, ya gabatar da takardar nadinsa ga ministan harkokin waje na Somalia, Abdirahman Mohammed Beileh a jiya Laraba, wannan shi ne matakin farko na kara bude ofishin jakadancinSin a Somalia, bayan an samu dakon kusan shekaru 23.
Sabon jakadan na Sin a Somalia, Wei Hongtian, ya gabatar da takardar nadi tasa ne a yayin wani buki a ofishin ministan harkokin wajen Somalia.
A jawabinsa, ministan harkokin wajen Somalia, Abdirahman mohammed Beileh, ya yaba da nadin jakadan kasar ta Sin, a inda ya ce, hakan wata alama ce, ta karin matakan tsaro da kuma huldar da kasar ke yi da kasashen duniya. (Suwaiba)