Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang ya gana da takwararsa kuma ministar harkokin wajen kasar Somaliya, madam Fawzia Yusuf Haji Adan a ranar Litinin a nan birnin Beijing. A yayin tattaunawar tasu, mista Wang ya yi tadi kan dangantakar gargajiya dake tsakanin kasashen biyu tare da jaddada kasar Sin za ta cigaba da tallafawa tsarin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.
Kuma kasar Sin a shirye take wajen kara karfafa cudanya tsakanin manyan jami'ai, da cigaba da fadada huldar gaskiya tare da kasar Somaliya a fannoni daban daban da kuma taimakawa wannan kasa wajen kokarin cimma zaman lafiya da zaman jituwa mai dorewa, in ji mista Wang. A nata bangare kuma, madam Fawzia ta bayyana kasar Somaliya na maida kasar Sin a matsayin kawarta da kuma abokiyar hadin gwiwa ta kwarai domin haka, Somaliya na fatan cigaba da tafiyar dangantaka a fannonin da suka hada da makamashi, gine gine, noma da tsaron kasa tare da kasar Sin.
Madam Fawzia ta iso nan kasar Sin a ranar 22 ga watan Agusta a cikin wani rangadin aiki da zai kare ranar Laraba. (Maman Ada)