Ministan lafiya na Nigeriya, Onyebuchi Chukwu ya ce, ta yiwu Najeriya ta kasance cikin barazana ta kwayar cutar cutar Ebola, mai saurin yaduwa, wacce a halin yanzu ke yin barna a kasashen Afrika ta yamma.
Ministan dai ya bayar da wannan gargadi ne, a yayin da yake jawabi, a karshen taron mako-mako na majalisar mulkin tarayyar kasar ta Najeriya.
Ministan ya kara da cewar, annobar cutar, wacce ke saurin hallaka mutane, na ci gaba da matsantowa ta bangaren yankin gabas zuwa Najeriya daga sauran kasashen Afrika ta yamma, da kuma kasashen Afrika ta tsakiya.
Ministan lafiya na Najeriya ya ce, kawo ya zuwa yanzu babu wata allurar rigakafi ko wani magani da ke murkushe cutar Ebola, inda ya kara da cewa, ma'aikatar lafiya na daukar matakan da suka dace, musamman wajen wayar da kan jama'a domin kaucewa bullar annobar a kasar.
Ministan ya jaddada mahimmancin dake akwai, na tabbatar da tsabta domin kare yaduwar cutar a Najeria. (Suwaiba)