A jiya Litinin ranar 16 ga wata ne kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi bikin zagayowar ranar yaran Afrika na shekarar 2014 a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Kungiyar tarayyar Afrika ta ce, ita wannan rana tana baiwa masu ruwa da tsaki a kan 'yancin yara, wadanda suka hada da gwamnatoci, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin kasa da kasa wata dama na duba al'amura da suka shafi yara.
An yi bikin a karkashin taken da ke cewa, "samawa yara ingantaccen ilmi kyauta a ckin wani yanayi na kawance ya zama dole ga daukacin yaran Afrika".
A cikin jawabinsa na bude taro, kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika a kan al'amuran jin dadin jama'a, Mustapha Sidiki Kaloko, ya jaddada cewar, kungiyar tana gudanar da bikin yaran Afrika a ranar 16 ga watan Yuni na ko wace shekara, domin tunawa da zanga-zangar shekarar 1976, wanda yaran makarantar Soweto dake Afrika ta Kudu suka yi a wancan lokaci.
Su dai yaran sun yi zanga-zanga ne a shekara ta 1976, domin nuna kin amincewa da irin ilmin da ake ba su, wadanda suka ce, an tsara shi ne, domin ya cimma muradun gwamnatin nuna banbancin launin fata ta wancan lokaci.
A shekarar 1991, babban taron kungiyar tarayyar Afrika ya amince da wani kuduri, wanda ya kebe ranar 16 ga watan Yuni na kowace shekara, a matsayin rana bikin yaran Afrika.
Daga cikin abubuwan da za'a gudanar a wajen bikin da ake gudanarwa na yau a can babbar hedkwatar kungiyar a Habasha, suka hada da wake-wake da yaran za su yi, da kuma wasan kwaikwayo da wasanni, har ma da wani fili na nuna albarkar fasaha na yara, da kuma wani dandalin na gabatar da tambayoyi da amsoshi a lokaci guda.
A yayin jawabinsa, shugaban kungiyar tsare-tsare ta duniya Nigel Chapman, ya lura da cewar, dukanin yara suna da 'yanci na samun ilmi kuma makomar Afrika da ta duniya baki daya ta dogara ne a kan falalar 'yancin na samar da ilmi ga daukacin yara. (Suwaiba)