in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
HCR ta bukaci Kenya kada ta kori 'yan gudun hijira
2014-04-18 14:26:49 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD HCR ta yi kiran kasar Kenya a ranar Alhamis kada ta kori 'yan gudun hijira da ta cafke a cikin shirinta na tsaro da take gudanar domin kawar da tsagerun mutanen da ake aikata munanan laifuffuka da 'ya ta'adda a cikin kasar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a Nairobi, hukumar HCR ta nuna damuwa game da tsare 'yan gudun hijira fiye da masu neman mafaka dubu guda da aka cafke a lokacin ayyukan yaki da ta'addanci da jami'an tsaron kasar Kenya suka gudanar a Nairobi tun ranar 2 ga watan Afrilu da kuma suka shafi 'yan kasashen wajen wadanda ba su da takardun zama.

HCR ta gamsu ta matakin da gwamnatin Kenya ta dauka na cewa, duk wani 'dan gudun hijira ko wani mai neman mafaka da aka yi wa rijista ba za'a kore shi ba nan take, amma duk da haka hukumar na nuna damuwa kan cewa, su ma sauran mutanen da aka kora za su iyar fuskantar barazana idan aka mai da su kasarsu.

Sanarwar ta HCR ta zo lokacin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya dauki alwashin cigaba da farautar 'yan ta'adda har sai ya kuftar da kasarsa daga wannan barazana. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China