Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da bangaren 'yan adawa sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ta tsagaita wutar yaki domin a samu daman gudanar da ayyukan mika kayayyakin agaji ga dimbin mutanen dake jiran taimako.
An dai samu kaiwa ga yarjejeniyar ne a karkashin shiga tsakani na hukumar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afirka IGAD, bayan da bangaren gwamnati da na 'yan tawaye suka komo da tattaunawa ta samar da zaman lafiya a ranar 28 ga Aprilu a birnin Addis Ababa, fadar gwamnatin kasar Habasha.
Shugaban tawagar gwamnatin Sudan ta Kudu Nhial Deng Nhial da kuma shugaban dake wakiltar bangaren 'yan adawa Janar Taban Deng, a wajen tattaunawar sulhun, sun rattaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta a inda kuma dukaninsu biyu suka sha alwashin za su girmama yarjejeniyar tare da aiki da ita. (Suwaiba)