Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana sunan Laftana janar, Yohannes Gebremeskel Tesfamariam, 'dan kasar Habasha a matsayin kwamandan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu UNMISS.
Kakakin babban sakatare na MDD ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya baiwa manema labarai cewar, Laftana janar Tesfamariam, ya gaji manjo janar Delali Johnson Sakyi, 'dan kasar Ghana, wanda ya kammala aikinsa a ranar 9 ga watan Yuni.
Sanarwar ta ce, Laftana janar Tesfamariam, kwararren ma'aikaci ne, domin ya yi shekaru 35, yana aiki da rundunar tsaron Habasha, ya kuma yi aiki da MDD a wuraren da ake rikice-rikice.
A kwanan nan ne Laftana Tesfamariam ya rike mukamin shugaban tawagar UNMISS da kuma rundunar tsaron MDD ta wucin gadi a Abyei. (Suwaiba)