A jihar Kaduna ta tarayyar Najeirya, an sanya dokar hana fita ta awowi 24, a wuraren da aka kai hare-hare, inda aka kashe mutane 38, a karamar hukumar Sanga dake jihar.
Shugaban karamar hukumar Emmanuel Adamu ya ce, hakan ya zama dole saboda hankulan jama'a sun tashi.
Harin da ake zargin Fulani makiyaya ne suka aiwatar da shi, a kauyuka guda biyu dake karamar hukumar Sanga a daren Litinin ya haifar da asarar rayuka, da kuma jikkata mutane da dama. (Suwaiba)