Shugaban karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, Emmanuel Adamu ya ce, wasu hare-hare kashi biyu da aka kai a jihar Kaduna dake tsakiyar arewacin Najeriya a daren Litinin ya haddasa asarar rayuka 38, kuma wasu mutane da dama sun sami rauni.
A yayin da yake magana ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban karamar hukumar ta Sanga ya ce, an kaddamar da harin ne a lokaci guda a kauyen Ankpon a yankin Nandu da kuma kauyen Kabamu dake Fadan Karshi a yankin Numana, dukaninsu a karamar hukumar Sanga dake jihar ta Kaduna.
Shugaban karamar hukumar ya ce, yana zargin Fulani makiyaya ne suka kai harin a wuraren biyu, harin nasu wanda ya kai wayewar gari, ya haddasa asarar rayuka 21 a Fadan Karshi, kuma an kashe 17 a Nandu Adamu.
Emmanuel Adamu, ya yi kira a kan jama'ar yankin da su kasance cikin natsuwa domin a yanzu an dauki matakan tsaro da za su iya dakatar da kashe-kashen da ake yi.
Hakazalika, gwamnan jihar ta Kaduna, Mukhtar Yero ya yi allah wadai da harin, tare da kira a kan mazauna kauyukan biyu da su kwantar da hankalinsu domin tuni aka tura jami'an tsaro a yankunansu domin tabbatar da doka da oda.
Yero ya ce, harin wani takalar fada ne da wadansu mutane wadanda ba su da kishin kasa suka aiwatar da zimmar tada zaune tsaye. (Suwaiba)