Daraktar hukumar shiga tsakani da wanzar da sulhu ta CCMA a Afirka ta Kudu Nerine Kahn, ta bayyanawa manema labaru kokarin da hukumar ta ke ci gaba da yi, wajen ganin an kawo karshen yajin aikin da ma'aikatan sashen hakar ma'adanin Platinum ke yi a kasar.
Kahn ta ce, kawo yanzu, CCMA na yunkurin ganin an cimma matsaya tsakanin kungiyoyin 'yan kwadago dake aikin hakar ma'adanin, da kuma manyan kamfanonin hakar Platinum din guda uku.
Yajin aikin da 'yan kwadagon kimanin su 80,000 suka shafe kusan makwanni uku suna gudanarwa dai, na da alaka ne da batun neman mai da mafi karancin albashi su zuwa Randi 12,500, kimanin dalar Amurka 1,130 a kowane wata da ma'aikatan suka bukata, kudaden da kamfanonin da suke wa aiki suka ce ba za su iya biya ba.
A ranar Laraba 5 ga watan nan ne dai CCMA ta dakatar da tattaunawar da take yi da jimillar masu ruwa da tsaki, domin samun damar ganawa da daidaikun su, duka dai da nufin shawo kan wannan batu cikin lumana.
Tuni dai wannan yajin aiki ya fara haddasa mummunan sakamako ga darajar kudin kasar Afirka ta Kudun, lamarin da masanan tattalin arziki ke kallo a matsayin wata babbar asara ga kasar.
Kazalika minista a ma'aikatar kula da ma'adanan kasar Susan Shabangu, ta bayyana cewa, yajin aikin da ma'aikata kan yi, ba shi da wani cikakken amfani gare su. Domin a cewarta, dokar hana ma'aikata samun albashi yayin da suke yajin aiki, kan hana su samun wata riba bayan janye yajin aikin. (Saminu)