A kalla 'yan kasuwa 25 ne suka rasa rayukansu, sakamakon wani hari da wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, suka kai wata kasuwa dake kauyen Daku a jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.
Wakilin kamfanin dillacin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, harin na ranar Lahadi, ya auku ne yayin da 'yan kasuwa, da sauran jama'a ke tsaka da harkokin su. Kaza lika shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi dirar mikiya ne a kasuwa, suka kuma yi harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane, tare da jikkata wasu da dama.
Bugu da kari an ce, maharan wadanda suka shiga kasuwar kan babura da wasu kananan motoci, sun fasa wasu runfuna, suka kuma wawashe kayan da ke ciki.
Shi dai kauyen Daku na karamar hukumar Askir Uba ne, mai nisan kilomita 30 daga Chibok, inda aka sace 'yan matan nan su sama da 200 daga makaranta cikin watan Afirilun da ya shude. (Saminu)