in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta samar da guraben aikin yi miliyan 1.8 ko wace shekara
2014-06-27 15:16:40 cri

A kokarin da take na magance matsalar talauci, gwamnatin Najeriya za ta bullo da guraben ayyukan yi, har miliyan 1.8 a ko wace shekara.

Ministan ciniki da saka jari na Najeriya, Olusegun Aganga, shi ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da injin din buga takardu a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.

Aganga ya ce, akwai bukatar ga Najeriya ta janyo hankalin saka jari daga kasashen ketare, tare da tallafawa kamfanoni na cikin gida ta hanyar sayen kayayyakin da suka sarrafa.

Ministan ya shaidawa taron manema labarai a Lagos cewar, Najeriya za ta iya kula da kamfanonin, tare da kare guraben ayyuka da ake da su a yanzu da kuma kirkiro da wasu guraben ayyukan yi.

Kamar yadda Aganga ya ce, gwamnatin Najeriya na sane da bukatar daukar mataki, har ma ta fara bullo da wasu manufofi da shirye-shirye, da zimmar magance matsalar ta rashin aikin yi.

Ministan ya kara da cewar, daga cikin matakan da gwamnatin Najeriyar ke dauka na bunkasa ayyukan yi, gwamnatin ta janyo hankalin saka jari, mai darajar dalar Amurka biliyan 14, a bangaren albarkatun man fetur, kuma ya ce, daga cikin kudaden saka jarin da Nigeriyar ta samo, za'a yi amfani da dalar Amurka biliyan 9 a Lagos. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China