Helkwatar tsaron tarayyar Najeriya ta ce, ta samu nasarar cafke daya daga manyan jagororin kungiyar nan ta Boko Haram, wanda ake nema ruwa a jallo, yayin wani bincike na tantance mutane 486 da jami'anta suke tsare da su.
Wata sanarwa daga rundunar sojin ta rawaito kakakin manjo janar Chris Olukolade, na cewa, an damke mutumin ne a kan hanyarsa ta zuwa birnin Fatakwal daga Enugu, a daren ranar Lahadin da ta gabata.
Shi ma kwamandan bataliya ta 144, ta rundunar sojin Najeriyar laftana Kanar Rasheed Omolori, ya shaidawa manema labaru cewa, jami'ansa, sun cafke mayakan kungiyar Boko Haram su 486, dake cikin wani jerin gwanon motoci 33.
Wadanda ake zargin dai na tsakanin shekaru 16 zuwa 24 ne da haihuwa, sun kuma ce, suna kan hanyarsu ce, zuwa kudancin kasar domin neman ayyukan yi. (Saminu)