Kotun koli ta kasar Libya ta yanke hukunci a kan cewar, zaben sabon firaministan kasar Ahmed Maitiq, ya sabawa kundin tsarin mulki na kasar. Wannan yanke hukunci ya kawo karshen tababar da aka yi makonni da dama da suka gabata, a kan shin wane ne takamaiman firaministan kasar ta Libya.
Wata majiya daga babban ofishin kotun koli ta kasar, ta shaidwa kamfanin dillanci na labarai cewar, kotun ta gabatar da karya dokoki da aka yi a lokacin zaben, kuma daga bisani sai ta yanke hukunci cewar, kada kuri'ar majalisar dokokin kasar ya sabawa kundin tsarin mulki na Libya.
A wani mai da martani da ya yi, sabon firaministan wanda aka soke zaben shi, Maitiq ya ce, zai girmama hukuncin kotun, kuma zai sauka daga mukamin nashi, a inda ya yi fatan, matakin da ya dauka zai tunatar da 'yan siyasar kasar ta Libya, da su dinga girmama tsarin doka. (Suwaiba)